Har yanzu wasu daga cikin gidajen man yan kasuwa basu fara siyar da litar fetur akan farashin da IPMAN tayi alkwari ba na naira 935.
Idan za’a iya tunawa shugaban ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu, IPMAN a matakin ƙasa, Maiganfi Garima ne ya bayyana cewa ƴan kasuwar zasu fara sayar da litar man fetur kan farashin Naira 935, daga yau litinin 23 ga watan Disamba.
Sai dai wani rangadi da wakilan Daily News 24, suka gudanar a safiyar yau sun iske ana siyar da litar man akan farashin naira 1080, a wasu gidajen man yan kasuwa a birnin Kano.
Sannan an fara ganin karuwar layukan ababen hawa a gidajen man, ba kamar kwanakin baya ba, da ba’a samun yawaitar masu shan man.
Bisa ga bincike kawo yanzu ba’a samu wasu gidajen man yan kasuwar da suka yi biyayya ga bayanin shugaban kungiyar ta IPMAN ba saboda suna siyar da litar man ne akan farashin daya zarce daira dubu guda.
Rage farashin da aka sanar ya biyo bayan yadda matatar fetur ta Dangote, ta sanar da rage farashi ga yan kasuwa zuwa naira 899, wanda bayan haka shima kamfanin NNPCL, ya rage nasa farashin zuwa 899, saboda saukakawa yan kasa suyi bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara a cikin sauki.