Tinubu zai gana da yan jarida da karfe 9 na daren yau

0
47

Shugaban kasa Bola Tinubu, zai gana da yan jarida a karon farko tun bayan hawan sa karagar mulkin Nigeria a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2019.
Kafafen yada labarai na kasa da suka hadar da NTA da FRCN zasu yada tattaunawar kai tsaye.

Mai magana da yawun Shugaban Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan a yammacin yau litinin.

Ana kyautata zaton cewa tattaunawar zata shafi yanayin tafiyar gwamnatin Tinubu kusan tsawon shekara biyu.

Fannin tsaro, da tattalin arziki na daga cikin bangarorin da ake ganin tattaunawar zata mayar da hankali.

Za’a fara yin hirar da misalin karfe 9 na daren yau litinin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here