Shugaban Nigeria Bola Tinubu, yace babu gudu babu ja da baya akan kudurin dokar harajin daya aikewa majalisa.
Ya bayyana haka ne a daren ranar Litinin yayin tattaunawa da kafafen yada labarai da tashar talbijin ta kasa NTA ta watsa.
Kudirin sake fasalin harajin da ke gaban Majalisar ya haifar da cece-kuce tare da rashin samun goyon baya musamman daga shugabannin arewa, lamarin da ya tilastawa ‘yan majalisar tuntubar juna da dakatar da tattaunawa akan kudurin dokar don tattaunawa da fannin shari’a akan dokar, kamar yadda shugaban kasa ya bayar da umarni.
Amma Tinubu a cikin jawabinsa na yau ya ce gyare-gyaren watakila ba kowa ne zai amince da su ba, amma duk da haka babu abinda zai hana aiwatar da dokar.
A cewar Tinubu, an kirkiro gyaran dokar harajin don taimakawa talakawa, da kuma fadada hanyoyin samun haraji, ta yadda za’a iya samun karin mutanen da zasu rika biyan haraji.
Shugaban Nigeria Tinubu, yace alamar shugaba nagari ita ce, yin abin da ya kamata a lokacin da ya dace, ma’ana yanzu shine lokacin daya kamata yayi gyara a fannin harajin da ake cewa zai karawa talakawa kunci.