K
Ƙungiyar dillalan man fetur ta Najeriya, IPMAN da kuma kamfanin mai na ƙasa wato NNPCL , sun ce za su ci gaba da sayar da man fetur a tsohon farashi har zuwa lokacin da tsohon kayan da suke da shi zai ƙare.
Kamfanin na NNPCL dai ya ce a sabon farashin zai riƙa bai wa dillalan, man kan naira 899 inda su kuma za su sayar a kan naira 935.
Ƙungiyar dillalan man ta ce a yanzu haka tana ci gaba da tattaunawa da matatar Dangote domin ganin yadda za su soma ɗaukar man a sabon farashin, kamar Alhaji Salisu Ten-Ten, shugaban dillalan na shiyyar arewa maso yamma ya bayyanawa BBC.
Idan za’a iya tunawa dai a makon daya gabata ne kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN tace za’a fara siyan man fetur a farashin naira 935 daga ranar litinin data gabata.
Sai dai hakan bai kasance ba yayin da aka rika siyan man akan farashin naira dubu sa naira 70, zuwa da naira 80.
Amma daga baya NNPC ya rage farashin zuwa 935, a birnin tarayya Abuja.