Shugaban Nigeria Bola Tinubu, ya mika sakon taya murnar kirsimeti ga mabiya addinin kirista dake fadin duniya, inda ya nemi a nunawa juna kauna, da zaman lafiya yayin bukukuwan.
Cikin sakon da ya fitar a jiya Talata, Tinubu, yace kirsimeti lokaci ne na bayyana zaman lafiya da hadin kai.
Yace yana taya mabiya addinin kirista murnar zagayowar ranar da aka haifi Annabi Isa.
Suma a nasu bangaren shugabannin majalisun dokokin kasa Godswill Akpabio, da Tajuddeen Abbas, sun taya Kristocin Nigeria murna.