Mahaifiyar Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ta rasu.
Hajiya Maryam Namadi Umar, ta rasu a yau laraba.
Bayanin rasuwar ya fito cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Hamisu Mohammed Gumel ya fitar.
Sanarwar ta Æ™ara da cewa za a jana’izarta da misalin Æ™arfe 4:30 na yamma a Kafin Hausa.