Tinubu da Buhari basa faɗawa yan Nigeria gaskiya—Sule Lamido

0
23

Tsohon gwamnan jihar Jigawa Kuma daya daga cikin manyan jam’iyyar PDP, Sule Lamido ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da ta Muhammadu Buhari, data shude da rashin gaya wa ‘yan ƙasa gaskiya game da yanayin gudanar da gwamnatocin su.

Cikin wata hira da BBC, toshon gwamnan na jihar Jigawa ya ce gwamnatocin biyu sun fifita farfaganda a maimakon faɗa wa ‘yan ƙasa gaskiyar halin da ƙasar ke ciki.

Sule Lamido ya ce a shekarar da ta gabata gwamnatin Tinubu ta yi kasafin kuɗi na kusan Tiriliyan 30, kuma hukumomin tattara haraji na ƙasa sun ce sun tara naira tiriliyan 50, amma duk da haka gwamnatin Tinubu ta buƙaci cin bashin domin cike giɓi a kasafin kuɗin shekarar da ta gabata, inda yace kamata yayi a samu raguwar naira triliyan 20.

Sule Lamido, ya kara da cewa jam’iyyar APC mulkin yaudara take gudanarwa a Nigeria ba gaskiya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here