Gwamnatin tarayya zata gina jami’a a kudancin Kaduna

0
54

Shugaban Nigeria Bola Tinubu, ya amince a samar da sabuwar jami’ar gwamnatin tarayya a kudancin jihar Kaduna

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ne ya bayyana hakan yana mai cewa bayan jami’ar a yanzu haka gwamnatin tarayyar na tattaunawa akan yadda za’a samar da cibiyar kula da lafiya a Kafanchan duk dai a Kaduna.

:::Shigo da abinci daga ketare ne zai kawo sauki a Nigeria–inji Kungiyar Manoma ta AFAN

Shettima, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwar da mai magana da yawun sa Stanley Nkwocha, ya fitar ranar litinin, inda yace mataimakin shugaban ya tabbatar da wannan cigaba a ranar lahadin data gabata lokacin da yakai ziyarar ta’aziyya ga iyalan malamin addinin krista Mathew Hassan Kukah, bisa wata rasuwar da akayi musu, ta sarki Yohanna Sidi Kukah.

Shettima, ya fadawa al’ummar yankin Kaduna, cewa Tinubu, yana da burin inganta cigaban kudancin Kaduna,har ma yace nadin da aka yiwa Christopher Musa, a matsayin babban hafsan sojin kasa ya tabbatar da cewa shugaban kasar yana son tabbatar da tsaro a yankin.

Ya kuma ce gwamnatin tarayya zata cigaba d hada kai da gwamnatin jihar Kaduna don inganta kudancin jihar, inda yayi amfani da ziyarar wajen yabawa Gwamna Uba Sani, bisa yadda yake gudanar da mulkin sa.

Babban jagoran kristotcin, Kukah, ya bayyana jin dadin sa akan ziyarar Sshettima, a madadin daukacin iyalan su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here