Gwamnan Adamawa ya nada sabbin sarakuna 7

0
40
FINTIRI
FINTIRI

Gwamna Ahmad Fintiri na Jihar Adamawa ya naɗa sabbin sarakuna da hakimai bakwai a masarautun Jihar.

Gwamnatin Adamawa, ta sanar da cewa naɗin sabbin sarakunan ta fara aiki nan take bayan sanar da mutanen da aka bawa mukamin.

Sabbin sarakunan su ne Alhaji Sani Ahmadu Ribadu a matsayin Sarkin Fufore, da Ahmadu Saibaru a matsayin Sarkin Maiha, da Barista Barrister Alheri B. Nyako a matsayin Tol Huba da Farfesa Bulus Luka Gadiga a matsayin Mbege Ka Michika.

Sauran su ne Dakta Ali Danburam a matsayin Ptil Madagali, da Aggrey Ali a matsayin Kumun Gombi, da John Dio a matsayin Gubo Yungur.

Gwamnan ya bayyana cewa an zaɓo su ne bisa cancanta da farin jininsu, tare da taya su murna game da sababbin matsayin da suka samu.

Ya kuma nemi suyi kokarin samar da adalci a shugabancin su, da kawo wa al’ummar su cigaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here