Wani magidanci ya yankawa ‘yar da aka haifa masa akuyar sata ta dubu dari 2

0
61

Jami’an ofishin yan sandan Odeda, dake jihar Ogun, sun kama Wani mutum mai suna Akintoye Waris, bisa zargin sa da sace akuyar da darajar Kudin ta takai naira dubu dari 2, tare da yanka ta a lokacin shagalin bikin sunan ‘yar da aka haifa masa.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Omolola Odutola, ce ta sanar da hakan a yau inda tace an kama mutunin a ranar 2 ga watan da muke ciki, tare da wani mai suna Ajayi Yusuf.

Wanda ake zargin, ya saci akuyar a wani gidan gona mallakin wani mutum mai suna Mark, a ranar 25 ga watan Disamba daya gabata.

Rundunar yan sandan tace wanda ake zargin ya tabbatar da aikata laifin da ake bincikar sa, sannan yace ya yanka akuyar a ranar 27 ga watan Disamba, saboda shagalin sunan’yar da aka haifar masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here