Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya kori kwamishinonin sa biyar, a wani yunkuri na yin garambawul ga majalisar zartarwa ta Bauchi, da inganta ayyukan gwamnati.
Mai taimakawa gwamnan a fannin kafafen yada labarai, Muhktar Gidado, ne ya sanar da hakan a yau Talata cikin wata sanarwa daya fitar a birnin Bauchi.
Kwamishinonin da abin ya shafa sun hadar da kwamishinar ilimi Dr. Jamila Dahiru, Abubakar Bununu, kwamishinan tsaron cikin gida, Usman Dan Turaki, kwamishinan yada labarai, Farfesa Simon Yalams, kwamishinan noma, da kuma kwamishinan harkokin addini Yakubu Hamza.
Gidado, yace gwamna Bala Muhammad, yayi haka don Samar da mafita akan matsalolin da ake samu a wasu bangarorin tafiyar da gwamnatin sa, da kuma kirkiro sabbin hanyoyin cigaba.
Gwamnan Bauchi, ya kuma yabawa tsaffin kwamishinonin bisa rawar da suka taka a fuskar bunkasar cigaban Bauchi, lokacin da suke rike da mukamai.
Daga nan kuma gwamnan ya mikawa majalisar dokokin jihar, sunayen mutane 8 da yake so a amince ya nada su mukaman kwamishinonin.
Mutanen da za’a nada sun hadar da Isa Tilde, Abdullahi Mohammed, Dr. Bala Lukshi, Usman Shehu, Iliyasu Gital, Prof. Titus Ketkukah, Adamu Gabarin, sai kuma Dr. Mohammed Lawal.