Mai bawa Gwamnan Kano shawara ya rasu bayan rantsar da shi

0
48

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya mika sakon ta’aziyyar sa ga iyalai da yan uwan sabon mai bashi shawara a fannin ayyuka, Injiniya Ahmad Ishaq Bunkure, wanda ya rasu kwana É—aya bayan da gwamnan, ya rantsar da shi.

Mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ne ya sanar da hakan, yana mai cewa marigayin ya rasu a yau Laraba a kasar Masar.

Gwamna Yusuf, ya bayyana mutuwar Injiniya Ahmad, sa matsayin babban rashi ga iyalinsa da Kano baki É—aya.

Sanarwar tace Injiniya Bunkure mutum ne mai hazaƙa da sanin makamar aiki wanda jihar Kano za ta amfane shi.

Daga karshe Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, yayi addu’ar Allah ya gafarta masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here