An saka ranar daura auren G-Fresh da Alpha Charles

0
55

Jarumin Tik-Tok, G-Fresh, ya sanar da cewa a yanzu haka sun samu fahimtar juna tsakanin sa da masoyiyar sa Alpha Charles, bayan sun samu tangarda a kwanan nan.

An gano wani faifan bidiyon da masoyan suke rungume da juna, inda G-fresh, ya nemi masoyan sa suyi hakuri akan wasu kalaman da yayi a baya bayan nan.

:::‘Yan ta’adda sun sace mutane 46 a jihar Zamfara

  • Ya nemi afuwar waÉ—anda suka É“atawa rai, tare da sanar da su cewa an sanya ranar bikin su a ranar Asabar.

A ranar Talata, G-Fresh ya fito a bidiyo, inda ya nuna cewa lamarin aurensu da Alpha yana cikin matsala, kuma akwai yiwuwar a dakatar da shi.

Sai dai a ranar Laraba, G-Fresh, ya kawo ƙarshen wannan magana, inda ya bayyana cewa yanzu komai ya dawo daidai.

Yace bikin zai kasance tsakanin sati huÉ—u zuwa wata É—aya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here