Yan ta’adda sun kashe mutane 30 da suka je gaisuwar mutuwa a Katsina

0
28

Wasu yan ta’addan jihar Katsina sun kashe wasu mutane da suka je yin gaisuwar mutuwa su 30 a ƙauyen Baure da ke Ƙaramar Hukumar Batasri.

Masu gaisuwar ta’aziyyar sun hada da ’yan banga, yayin da suke kan hanyar su ta komawa gida a lokacin da ’yan ta’addan suka kai musu harin kwanton ɓauna inda nan take suka kashe mutum 15.

Shaidu sun bayyana cewa mutanen da harin ya rutsa da su sun je ta’aziyya daga ƙauyukan ƙananan hukumomin Safana da Kurfi da Charanchi da Kaita.

Sun shaida wa Aminiya cewa mutum sama da 30 ’yan bindigar suka kaiwa harin a yankin Ɓaure, wanda ya yi ƙaurin suna a ayyukan ’yan bindiga, tun ranar Talata amma sai ranar Alhamis aka samu labarin.

Rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar da harin, amma ta ce tana ci gaba da tattara bayanai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here