Kotun daukaka kara da ke Abuja ta bayar da umarnin sake sauraron shari’a kan rikicin masarautar Kano da ya hada da Alhaji Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi.
Kotun daukaka kara, a hukuncin da ta yanke a yau, ta ce ba’a yi wa Sanusi adalci ba saboda yadda wata babbar kotun Kano ta gudanar da shari’a a kansa.
Mai shari’a Mohammed Mustapha wanda ya yanke hukuncin, ya bayyana cewa babbar kotun Kano ba ta yi wa Sanusi adalci ba ta hanyar gudanar da shari’a ba tare da bashi damar bayanin nasa bangaren ba.
Mai shari’a Mustapha ya ce ya zama wajibi dukkan kotuna su tabbatar da adalci ga kowane bangare ta hanyar ba su dama daidai gwargwado, ya kara da cewa yadda aka gudanar da shari’ar ya zama cin zarafi ga Sanusi.
Domin haka kotun daukaka kara ta bayar da umarnin a mika karar ga babban alkalin alkalai na jihar Kano domin baiwa wani alkali damar yanke hukuncin adalci cikin gaggawa.