Mahukuntan birnin Los Angeles na kasar Amurka sun umarci mutanen da suka zarce 144,000 su bar gidajen su saboda gobarar dajin da ke ci gaba da yi wa yankin barazana.
Cikin wani saĆ™o da ofishin gwamnan jihar ya wallafa a shafin sa na X, ya ce hukumomi sun tanadi wurare takwas domin tsugunar da mutanen da suka bar gidajen su saboda iftila’in gobarar.
Kawo yanzu an samu fiye da mutane 700, dake zaune a matsugunan.
Zuwa yanzu gobarar ta yi ajalin mutum 11.
Iska mai Ć™arfi da ake samu a Los Angeles na kawo koma baya ga Ć™oĆ™arin kashe gobarar da jami’ai ke yi.