An bayar da rahoton mutuwar mutane da yawa a kauyen Kakindawa, dake karamar hukumar Maradun, a jihar Zamfara, sanadiyyar harin jirgin sojojin Nigeria.
Wani mutum mai suna Garba Umar, mazaunin kauyen ya sanar da jaridar Punch, cewa lamarin ya afku a jiya asabar lokacin da yan sa-kai ke kokarin kaiwa mutanen kauyen Tungar Kara, dauki sakamakon harin da yan bindiga suka kai musu a lokacin.
Yace yan Bijilanti, sun taru domin kaiwa mutanen dauki, bayan samun rahoton cewa yan bindiga sun je yankin suna sace dabbobi da kuma kokarin sace mutane.
Garba, yace a lokacin da ake kokarin kaiwa mutanen kauyen Tungar Kara dauki, da misalin karfe 3:30, na yamma sai ga jirgin sojojin Nigeria ya fara jefawa yan Bijilantin Bama bamai, kuma daga haka ne yan ta’addan suka samu damar tserewa dazuka.
Mutumin, yace aƙalla mutum 16, sojojin suka kashe ciki har da dan cikin sa.
Yace sun tattaru domin ceton makobtan su, sai sojoji suka kashe su maimakon su kashe yan ta’adda, yana mai cewa hakan abin karya zuciya ne.
Sai dai mai magana da yawun, rundunar sojin dake atisayen Fansan yamma, Laftanar Kanar, Abubakar Abdullahi, yace zai binciki zargin, da Kuma yin karin bayani.
Wannan dai ba shine karon farko, da ake samun sojoji da kuskuren jefawa fararen hula bama bamai, wanda hakan ya faru, a jihohin Kaduna, Katsina.