SDP tace bata da wata alaka da Atiku ko El-Rufa’i akan zaben shekarar 2027

0
51

Jam’iyyar SDP tace bata da yarjejeniyar hadakar siyasa tsakanin ta da Atiku Abubakar da El-Rufa’i, akan zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Shugaban jam’iyyar na kasa Alhaji Shehu Gabam, ne ya bayyana hakan, inda yace SDP bata da wata alaka da dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP, a zaben shekarar 2023, Atiku Abubakar da El-Rufa’i, gabanin zaben shekarar 2027.

Gabam, yace a yanzu babban abin dake gaban su shine gina jam’iyyar don samar wa Nigeria mafita akan matsalolin da take ciki.

Gabam, ya bayyana hakan a jiya lokacin da ake zantawa dashi a talbijin ta Channels, a daren lahadi.Yace kawo yanzu SDP bata da wata maganar yin hadaka da kowa.

Da yake jawabi dangane da ganawarsa da El-Rufai, Gabam, ya bayyana shi a matsayin mutum mai muhimmanci wanda yake da tasiri a siyasar Nigeria.

Sai dai ya nesanta jam’iyyar SDP daga duk wata alaka ta siyasa da tsohon gwamnan Kaduna.

Shugaban, SDP, yace alakar sa da El-Rufa’i, bata siyasa bace.

Amma ya ce jam’iyyun APC da PDP, sun gaza, sannan ya nemi yan Nigeria su tabbatar anyi komai a bayyane a Gwamnatin Tinubu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here