Amurka tace za’a tsagaita wuta a yakin da Isra’ila ke yi da Falasdinawa

0
64

Kasar Amurka tace nan bada jimawa ba, za’a cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a yakin kasar Isra’ila da Falasdinawa.

Mai bawa shugaban Amurka shawara akan harkokin tsaro Jake Sullivan, ya sanar da yan jarida cewa ana samun cigaba mai kyau a tatttaunawar sulhu dake wakana tsakanin Isra’ila da Hamas.

:::Cutar murar tsuntsaye ta shiga jihar Kano

Tuni wakilan Isra’ila da Hamas, suka karbi wani kundin yarjejeniyar sulhu a jiya litinin, sannan ana kyautata zaton cewa zasu sake ganawa a yau talata don yanke hukunci dangane da amincewa da yarjejeniyar tsagaita wutar wanda za’a tattauna a birnin Doha na Qatar.

Wakilin BBC ya ce yarjejeniyar ta yi bayanin cewa Æ™arin taimakon jin Æ™ai zai fara shiga Gaza kai tsaye, sannan sojojin Isra’ila za su fice daga yankunan da ke da yawan jama’a, kuma za su saki fursunonin FalasÉ—inawa dubu guda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here