Mutane miliyan 18 sun yi aikin Umrah a shekarar 2024

0
31

Gwamnatin kasar Saudiyya ta sanar da cewa an samu adadin mutane fiye da miliyan 18, wanda suka yi ibadar Umrah, a shekarar 2024, da hakan ya zama wani babban abin tarihin da bai taba faruwa ba a baya.

Ministan aikin Hajji da Umrah, na Saudiyya, Dr. Tawfiq Al Rabi’ah, ne ya shaida hakan a kasar.

Daga cikin mutanen akwai miliyan 16, da dubu dari 9, da suka gudanar da zallan aikin Umrah, sai mutane miliyan 1, da dubu dari 6, da suka yi aikin hajji, daga sassan duniya, a lokacin aikin hajjin bara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here