Ya kamata a mayar da rigakafin ciwon hanta dole—Majalisar wakilai

0
70

Majailsar wakilai ta nemi gwamnatin tarayya, ta hannun ma’aikatar lafiya ta tilasta yin gwaji da rigakafin ciwon hanta ga yara yan kasa da shekara 5.

Mambobin majalisar sun ce haka ne zai rage saurin kamuwa da kuma yaduwar cutar a tsakanin al’umma.

:::Mutane miliyan 18 sun yi aikin Umrah a shekarar 2024

Yan majalisar sun yanke wannan matsaya a yayin zaman su na yau Talata, bayan dan majalisa Kwamoti Laori, na jami’yyar PDP, daga jihar Adamawa, ya gabatar da kudirin.

Dan majalisar yace ciwon hanta cuta ce mai hadari da kuma haduwa tsakanin mutane, musamman daga mahaifiya zuwa jaririn ta lokacin haihuwa.

Bayan haka ana iya kamuwa da cutar wajen saduwar aure, ko wata ma’amalar jini tsakanin mai cutar da wanda baya dauke da ita.

Haka zalika akwai nau’in cutar da ake iya kamuwa da shi, ta hanyar taba duk wani ruwa daya fito daga jikin mai cutar, wanda haka ne yasa cutar ke yaduwa, da kuma hallaka mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here