Gwamnan Zamfara ya gana da masu binciken harin sojoji daya kashe fararen hula

0
34

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya gana da tawagar rundunar sojin saman kasar nan (NAF) da aka tura domin gudanar da bincike kan harin sojin sama na baya-bayan nan da ya faru a jihar, kuma yayi sanadiyyar mutuwar mutane yan babu ruwa na.

Gwamnan ya tarbi tawagar, karkashin jagorancin Edward Gabkwet, daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin sama.

A wata sanarwa da Olusola Akinboyewa, daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojin sama, ya fitar, ya ce Gabkwet ya shaida wa gwamna Lawal, cewa rundunar sojin sama ta jajirce wajen bin ka’idoji da tabbatar da gaskiya a duk ayyukanta, don ganin an tabbatar da komi ya tafi yadda ya kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here