APC ta dage ranar fara yakin neman zabenta

0
89

Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya dage fara yakin neman zaben da aka shirya kaddamarwa a ranar Laraba.

Darakta-Janar na kwamitin yakin neman zaben Tinubu da Shettima, kuma gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

A cewarsa, an yi hakan ne domin daidaita jadawalin lokaci da jadawalin ayyuka ne domin ya yi daidai da harkokin duk masu hannu a cikin yakin neman zaben don samun nasararsa.

A cewarsa, nan ba da jimawa ba za a sanar da sabon lokacin da za a fara yakin neman zaben jam’iyyar.

Sanarwar ta ce; “Tun da farko mun shirya tattaki da addu’o’in zaman lafiya a ranar Laraba, 28 ga watan Satumba, 2022, don fara yakin neman zaben shugaban kasa na 2023 a hukumance. Mun kuma sanar da cewa mambobin kwamitin yakin neman zaben sun kai rahoto hedikwatar yakin neman zaben a ranar domin karbar wasikun nadi.

“Duk da haka, saboda fadada jerin sunayen don samun karin masu ruwa da tsaki da bukatun cikin gida a APC, mun yanke shawarar daidaita jadawalin wadannan ayyuka domin tabbatar da cewa kowa yana cikin jirgin kafin a fara ayyukan a hukumance.

“Saboda haka, ayyukan da aka sanar a baya na ranar 28 ga Satumba ba za su ci gaba da kasancewa ba.

“A matsayinmu na jam’iyya mai mulki kuma mafi inganci a Nijeriya, mun fahimci sadaukarwa da fahimtar dimbin mambobinmu wadanda suka fi son sadaukar da kansu don wannan gagarumin aiki da ke gabanmu. Hakan kuma ya nuna irin tsananin soyayyar da ‘ya’yan jam’iyyar ke yi wa ’yan takararmu

“Za a sanar da sabon kwanan wata da jadawalin abubuwan da za su faru nan ba da jimawa ba”.

Idan ba a manta ba ranar 28 ga watan Satumba, 2022, ita ce ranar da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), ta ware ta ga jam’iyyu da ‘yan takara don fara yakin neman zabe a hukumance.

 

LEADERSHIP