Rasha ta yi gargadin cewa, matakin da Amurka ta dauka na aikewa da karin agajin soji zuwa Ukraine na kara hadarin fadan soji kai tsaye tsakanin Rasha da kasashen Yamma.
Jakadan kasar Rasha a Amurka Anatoly Antonov, ya ce wannan barazana ce ga Moscow, yan mai bayyana Amurka a matsayin mai shiga cikin rikicin.
Tun da farko, Amurka ta sanar da wani tallafin soja na dala miliyan 625 ga Ukraine.
An yi la’akari da manyan makaman Amurka da suka taimaka wa Ukraine ta kara kaimi kan mamayar sojojin Rasha.
Sojojin Ukraine sun samu gagarumin ci gaba a yankin arewa maso gabas da kudancin kasar a cikin ‘yan makonnin nan.
Washington ta sadaukar da kusan dala biliyan 17 a matsayin tallafin soji ga Kyiv tun lokacin da shugaban Rasha Vladimir Putin ya mamaye Ukraine a ranar 24 ga Fabrairu.
A cikin wata sanarwa, Mista Antonov ya yi gargadin cewa matakin da Amurka ta dauka na ci gaba da turawa gwamnatin Kiev manyan makamai ne kawai ke tabbatar da matsayin Washington a matsayin mai shiga cikin rikicin.
Ya ce hakan zai haifar da tsawaita zubar da jini da karin hasarar rayuka.
Bayan da ta sha kaye a fagen daga a kasar Ukraine a ‘yan makonnin nan, Rasha ta sha alwashin kare kanta da dukkan hanyoyin da ta dace, ba tare da kawar da amfani da makaman nukiliyarta ba.
Har ila yau Moscow tana ci gaba da yunkurin mamaye yankuna hudu na Ukraine: Donetsk da Luhansk a gabas, da Kherson da Zaporizhzhia a kudu.