Rukunin farko na sojojin kawancen Rasha ya isa Belarus

0
98

Ma’aikatar tsaron Belarus tace rukunin farko na Sojojin Rasha na sabuwar rundunar hadin gwiwa da kasar ya isa Minsk a wannan Asabar.

Ma’aikatar ta kara da cewa, ayarin farko na jami’an tsaron kasar Rasha zasu hadu da takwarorinsu na Belarus domin aikin hadin guiwa na musamman don karfafa kariya da tsaron kan iyaka.

Hotunan ma’aikatar tsaron sun nuna yadda wasu matan Belarus sanye da kayan gargajiya suke yi wa sojojin tarba ta musamman suna raba musu biredi da gishiri.

Barazanar Ukraine

A ranar Litinin din da ta gabata shugaban Belarus Alexander Lukashenko ya yi ikirarin cewa Ukraine na shirin kai wa kasarsa hari tare da sanar da rundunar hadin gwiwa da Moscow.

Lukashenko ya zargi kasashen Poland da Lithuania da Ukraine da horar da masu tsattsauran ra’ayi a cikin Belarus “don shirya zagon kasa da hare-haren ta’addanci da kuma harin soji a kasar”.

Fargabar farmakin hadin guiwa

Wannan tura sojojin ya haifar da fargabar cewa sojojin Belarus za su iya hada kai da sojojin Rasha a farmakin da suke kai wa Ukraine.

A ranar Juma’a Lukashenko ya shaida wa ‘yan jaridun Rasha cewa sojojin Belarus dubu 70 za su kasance cikin  wannan rundunar ta hadin gwiwa da Rasha, sai da bai bayyana adadin sojojin Rasha da zasu shiga rundunar ba.