Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta faɗakar da gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi da ma shugabannin jama’a, musamman a jihohin Anambara, Delta, Kuros Riba, Ribas da Bayelsa, cewa ambaliyar ruwa na nan tafe a cikin makwanni masu zuwa, sannan ta yi kira a gare su da su shirya wa aikin kwashe jama’ar da ke zaune a yankuna da hanyoyin da ruwan ke bi.
Ministar ta faɗi haka ne a taron da ta yi da manema labarai a ranar Lahadi a Abuja domin bayyana masu ƙoƙarin da gwamnati ke yi na rage raɗaɗin bala’in ambaliya a ƙasar nan, wanda ta ce babbar matsala Hajiya Sadiya ta ce duk da gagarumin ƙoƙarin da ake yi na kauce wa matsalolin ambaliyar wannan shekarar ta 2022 kamar yadda Hukumar Nazarin Yanayi ta Nijeriya ta hango zai faru, gwamnatocin jihohi da dama ba su yi wani shiri dangane da ambaliyar ba, wanda hakan ya jawo babbar asarar rayuka da ɓarnata dukiyoyi.
Ta ce: “Abin baƙin ciki ne a ce an rasa rayuka sama da 603 ya zuwa yau 16 ga Oktoba, 2022. Jimillar mutum 1,302,589 su ka gudu daga muhallin su, mutum 2,504.095 abin ya shafa baki ɗaya, mutum 2,407 sun ji rauni, jimillar gidaje 82,053 sun rushe baki ɗaya, yayin da guda 121,318 su ka lalace a wasu sassa nasu. Hekta 108,392 ta gonaki ta lalace a wasu sassa yayin da hekta 332,327 ta salwanta baki ɗaya, wanda ya haɗa da hanyoyi da yawa da sauran muhimman ababen more rayuwa.