“Ni ‘yar Najeriya ce” – Matar sabon yariman Birtaniya, Meghan

0
76

Matar dan sabon yariman Birtaniya Meghan Markle, ta bayyana cewa gaurayen kwayoyin halittarta, sun gwaraya da Nijeriya inda tace kashi 43 cikin dari ita ‘yar Nijeriya ce.

Ta bayyana hakan ne a cikin wani sabon shiri na faifan bidiyo na musamman na Spotify, Archetypes, inda ta gaya wa jarumin fina-finai dan Nijeriya Ba’amurke Ziwe cewa ta gano asalinta ne bayan samun cikakken tarihinta “shekara biyu da suka gabata”.

Da aka tambaye ta ko ta san wace kabilar kakanninta suka fito, gimbiyar ba ta yi bayani kan hakan ba amma ta bayyana cewa za ta cigaba da binciken hakan

A baya can, Meghan ta yi magana game da kasancewarta tana da tushe daga ruwa biyu amma ba ta zurfafa bincike cikin asalin tushenta ba sai ‘yan kwana kin nan.