Napoli za ta iya kaiwa wasan karshe na gasar cin kofin zakarun turai – Klopp

0
103

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jurgen Klopp ya ce ba abin mamaki ba ne kungiyar Napoli ta samu nasarar kai wa wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai a bana.

Bajamushen ya bayyana haka ne, yayin taron manema labarai gabanin wasan da Liverpool za ta yi a yau Talata, inda za ta karbi bakoncin Napoli a filin wasa na Anfield.

A karawar farko da suka yi, Napoli ce ta lallasa Liverpool da kwallaye 4-1.

A cewar Klopp a halin yanzu za a iya cewa Napoli ta zarce duka wata kungiya a Turai karsashi, tare da buga salon kwallon kafa mai ban sha’awa.

Har yanzu dai Napoli ba ta yi rashin nasara ba a dukkanin wasannin da ta buga tun bayan fara kakar wasa ta bana, inda a gasar zakarun Turai ta ke da maki 15 cif-cif bayan buga wasanni biyar, yayinda Liverpool ke biye da ita da maki 12.