A shirye muke mu karbi Doguwa a NNPP – Kwankwaso

0
114

Dan takarar shugaban Kasa a jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyar a shirye take ta karbi Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Kabiru Alhassan Rurum, jigo a jam’iyyar kuma dan Majalisar Wakilai na mazabar Rano da Kibiya da Bunkure daga Jihar Kano.

Sannan ya ce, Kwankwaso ya kafa wani kwamitin mai karfi na mutane hudu domin su je su yi wa  Ado Alhassan Doguwan ta’aziyyar mahaifinsa da ya dade da rasuwa.

Hakan ya biyo bayan kalamai na baya-bayan nan da dan Majalisar ya yi na cewa rashin ta’aziyyar ce ta sa su ka bata da Kwankwaso, a cikin jerin kalaman dan majalisar yake yi na bara’a ga jam’iyyarsa ta APC.

‘Yan kwamitin da Kwankwaso ya kafa sun hada dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a NNPP, Rufa’i Sani Hanga da Shugaba NNPP na Kano, Umar Haruna Doguwa da Sarki Aliyu Daneji da kuma  shi Kabiru Alhassan Rurum din.

Tun bayan da suka samu sabani a jam’iyyarsu ta APC, Shugaban Masu Rinjayen ake jin ya na furta wasu kalamai na yabon Kwankwaso da wasu ke cewa, angulu ce ke shirin komawa gidanta na tsamiya.

A farkon makon nan ne dai labarin wata sa-in-sa tsakanin Doguwa da dana takarar Mataimakin Gwamnan Kano na APC, Murtala Sule Garo, yayin wani taro a gidan dan takarar Gwamnan APC, Nasiru Yusuf Gawuna.