“Sannan ya sanya harajin mako-mako ga duk muhimman sassan da manyan ofisoshin ’yan sanda ke karkashin rundunar abin da ya fusta shugaban ’Yan Sandan Najeriya.”
Aminiya ta samu rahoto cewa mataimakan Kwamishinan ’Yan Sanda da aka sauya wa wurin aiki ne suka aike wa shugaban ’yan sanda rahoton rashawar da ke gudana a karkashin sabon kwamishinan.
Bayan nan ne Hedikwatar ’Yan Sanda ta Najeriya ta sa a yo binciken kwakwaf a sirrance, wanda a karshe ya tabbatar da zargin da ake wa sabon kwamishinan.
Wata majiya mai tushe ta ce Shugaban ’Yan Sandan da kansa ya zauna da wasu daga cikin masu zargin, a lokacin binciken, da nufin gano gaskiya.
A watan Agusta ne dai aka tura CP Abubakar Lawal zuwa Jihar Kano, bayan magabacinsa, ya yi ritaya daga aiki.
Wakilinmu ya nemi karin bayani kan lamarin daga kakakin ’yan sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi, amma ya ce ba shi da masaniya.
A halin da ake ciki ranar Litinin sabon kwamishin da aka tura Kano, Aliyu Garba, zai fara shiga ofis.