Labaran NPOWER da NASIMS a yau Talata

0
113

An bukaci masu cin gajiyar Npower da su kwantar da hankalinsu yayin da aka fara biyan kudin alawus din watan Agusta.

Nasims ya bayyana haka ne a dandalinshi na sada zumunta kamar haka;

Bayan tambayoyi da yawa game da sahihancin labaran biyan kuɗi na watan Agusta da ke yaɗuwa, ya zama dole mu share muku tantama.

Da fatan za a karɓi wannan bayani azaman tabbaci na hukuma na biyan kuɗin watan Agusta.

Haka zalika, ana ƙididdige asusun ku don biyan kudin watan Agusta kuma ana yin shi ne a hankali.

Idan biyan kuɗin ku yana kan shigowa, ku ci gaba da hakuri ku jira naku biyan.

Hakurin ku zuwa yanzu mun ya ba dashi sosai.

Mun gode!