Sake fasalin Naira: Mayakan ISWAP sun koma amfani da kudin Nijar

0
130
Majalisar Shura ta kungiyar ’yan ta’adda ta ISWAP, ta haramta karbar Naira daga hannun manoma da masunta, biyo bayan matakin da Gwamnatin Najeriya ta dauka na sake fasali takardun kudin.A kwanakin baya ne dai Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa ta yanke shawarar sake fasalin takardu na N200 da N500 da kuma N1000, wadanda za ta fara fitar da su nan da watan Disamba, sannan a ranar 31 ga Janairun 2023, za a daina karbar tsoffin takardar Naira.

Sai dai bayanai na nuna cewa wannan mataki ya jefa mayakan ISWAP a yankin Tumbus na tafkin Chadi da kuma nesanta daga rassan bankuna cikin rudani domin zai yi wuya su canza kudadensu zuwa sabbin takardun kudi.

Wata majiyar leken asiri ta shaida wa Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tayar da kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, cewa yanzu haka, ’yan ta da kayar bayan suna karbar kudin CFA na kasashen rainon Faransa na Afirka ta Yamma da suke niyyar maye gurbin Nairar Najeriya a matsayin kudin kasuwanci a yankin.

Majiyar ta kuma ce ’yan ta’addan sun kuma haramta wa duk wasu masunta da makiyaya da manoma shiga cikin tafkin Chadi ta hanyar Marte da Abadam da kuma Gamborun Ngala, domin hana Naira shiga sansanonin ’yan ta’addan da ke Tafkin Chadi.

Ibn Umar da Malam Ba’ana, kwamandojin tsagerun ISWAP masu kula da haraji da lauyoyi, wadanda suka kafa dokar, sun ce an bar mutanen ne kawai ta hanyar aminci da kungiyar ta’addanci ta kafa ta Bulgaram, Cikka, Guma, Maltam, Doron, Liman da Ramin Dorina, wasu kauyuka a Jamhuriyar Kamaru.

A maimakon haka, ISWAP na karbar CFA 1,500 a matsayin haraji kowane wata daga mutanen da suka nuna suna son biya.

Har ila yau, sun tabbatar da hanyoyin kasuwanci musamman don ba da dama ga ’yan kasuwar shigo musu da kayan abinci da man fetur da makamai da sauran kayan aiki.