Shugabannin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a duniya G20 sun bude babban taronsu wannan Talata a tsibirin Bali na kasar Indonessia, inda mai masaukin baki na neman hadin kai da kuma daukar kwararan matakai don daidaita tattalin arzikin duniya duk da rashin jituwar da ake fama da ita kan yakin Ukraine.
G20 da ta hada da kasashe daga Brazil zuwa Indiya, Saudiya da Jamus, na da sama da kashi 80 cikin 100 na yawan kayayyakin da ake samarwa a duniya, kashi 75% na cinikin kasa da kasa da kuma kashi 60% na al’ummarta.
Wata kyakkyawar alamar murmurewar duniya da aka gani tun a jajibirin taron ita ce ganawar da shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yi da takwaransa na China Xi Jinping na tsawon sa’o’i uku, inda shugabannin biyu suka yi alkawarin karfafa cudanya da juna duk da bambance-bambance da dama dake tsakaninsu.