Gwamnati ta bullo da tsarin koyarwa da harsunan gida a firamare

0
86

Majalisar ministoci ta amince da wata manufa kan amfani da harsunan kasar wajen koyar da dukkan daliban kasar a matakin firamare a fadin kasar.

Ministan Ilimi Adamu Adamu ne ya sanar da haka  ga manema labarai, bayan taron majalisar ministoci da aka yi a ranar Laraba cewa majalisar ta amince a aiwatar da sabon tsarin amfani da harsunan gida da ake kira National Language Policy wanda ma’aikatarsa ta kirkiro.

Ministan ya bayyana cewa ” ka’idojin koyarwa na shekaru shida na farko a makaruntun firamare za su kasance cikin harshen gida.”

Tun kafin  Najeriya ta samu ‘yancin-kai daga Birtaniya take amfani da Ingilishi  a matsayin  harshen hukuma inda cibiyoyin  ilimi a kowa ne mataki suke amfani da shi a matsayin harshen gama-gari na koyarwa.

Haka kuma wasu al’ummomi  na amfani da harsunan gida  tare da Ingilishi  a azuzuwa.

A yanzu mahukunta sun ce za a fi ba harsunan gida fifiko a makarantun  firamare.

A cewar ministan ilimin  Najeriya: ”Yara sun fi koyon abu da sauri, idan aka koyar da su a cikin yarensu na gida.”