Jerin wayoyin da ba a amince a yi amfani da su a Najeriya ba – NCC

0
83

Hukumar kula da sadarwa ta Najeriya, NCC, ta gargadi al’umma kan siyan wasu wayoyi da amfani da su don ba a amince da su ba.

Hukumar ta kuma sanar da babban hukunci da za ta yi kan yan kasuwa masu sayar da jabun wayoyi ga mutane.

NCC ta fitar da wannan sanarwar ne bayan tawagarta ta kama wani Yahaya Ado na Gezawa Communications Limited kan sayar da jabun wayoyin kamfanin Gionee.

Ado, ya kuma gaza nuna izini da ya samu daga hukumar na fara sana’ar wayoyi.

Hatsarin da ke tattare da amfani da wayoyin da ba a amince da su ba NCC, cikin sanarwar da ta fitar ta yi gargadin cewa amfani da wayoyi da ba a amince da su ba ka iya janyo wa masu amfani da su asara da rashin jin dadin amfani.

Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban sashin aiwatarwa na NCC, Mallam Salisu Abdu, wanda ya jagoranci tawgaar, ya nuna damuwarsa kan yadda wayoyin jabu suka cika kasuwar wayoyi da ke Beirut Street, Kano da wayoyin da ba a amince da su ba.

Ga jerin wayoyin da aka haramta amfani da su a Najeriya

Wayoyin Gionee masu samfurin G800, da L990 Wayoyin H-Mobile masu samfurin it5606+, da H351 Wayoyin FoxKong masu samfurin F30, da F300 Wayoyin KGTEL masu samfurin K2160 da KG1100.

Jerin wayoyin da aka amince da su

Kazalika, shafin NCC ya lissafa jerin wayoyi 1,891 daga kamfanoni daban-daban da aka amince yan Najeriya su yi amfani da su. Wayoyin da aka lissafo sun hada da na kamfanonin Nokia, Apple, Fero, Motorola, Huawei, LG, Samsung, Sony Ericsson, Itel da sauransu.

A bangare guda, Hukumar NCC mai kula da harkokin sadarwa a Najeriya ta ce ta gano wata mugunyar manhaja da ake amfani da ita don kutse don sace bayannan sirri na al’umma a wayoyin salula. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, sashen Computer Security Incident Report na hukumar ta NCC ne ya sanar da hakan.