Makarantar firamare mai malamai 2 kacal da adadin dalibai 544 a jihar Yobe

0
169

Duk da yawan ikirarin da gwamnatin jihar Yobe ta sha yi wajen inganta harkokin ilimi, kafa kwamitin sake farfado da fannin, wakilin mu ya gano wata makarantar firamare a kauyen Ngelshengele da ke karamar hukumar Fune a jihar; mai malamai biyu kacal tare da adadin dalibai 544 a ajujuwan makarantar.

LEADERSHIP Hausa ta jiyo ta bakin shugaban makarantar (Headmaster) Malam Sa’id Wakil, inda ya koka dangane da rashin malamai a makarantar, kana kuma al’amarin da ya ce yana daya daga cikin manyan kalubalen da Firamare ta Ngelshengele ke fuskanta. Inda ya ce malam

“Akwai wani malami daya wanda aka turo shi zuwa wannan makarantar, amma mun gano cewa dalibi ne daga Gashuwa. Sannan a gaskiya ban ma san shi ba, amma ko shakka babu zuwan sa zai taimaka.” inji shi.

Malam Sa’id ya ce, “Baya ga rashin malamai, kusan dukkan ajujuwan wannan makaranta na bukatar gyara. Kamar yadda kuke gani, duk sun lalace.”

Bugu da kari kuma, ya ce duk da an gyara wasu azuzuwan ne ta tallafin bankin duniya da kwamitin kula da makarantu (SBMC). Ya kara da cewa, kimanin N500,000 ne aka tara domin gyara wasu azuzuwan da daliban ke daukar darasi a halin yanzu.

 

LEADERSHIP