Qatar 2022: Faransa ta kora Poland gida da ci 3-1

0
69

Tawagar ’yan wasan Poland za su koma gida bayan Faransa ta casa su 3-1, ta kuma tsallaka zuwa Kwata-Fainal a wasansu na ’Yan 16 a Gasar Kofin Duniya da ke gudana a Qatar.

Kasar Faransa, mai kokarin kare lambu ta a gasar, ta ta caskara tawagar Poland ne a wasan da aka buga a Filin Wasa na Al-Thumama a ranar Lahadi.

Dan wasan Faransa, Oliver Giroud ne ya fara zura kwallo a ragar Poland a minti 44 da fara wasan.

Daga baya a minti na 74, Julian Mbappe ya sa kwallo ta biyu a ragar Poland.

Da haka yanzu Mpabbe mai shekara 23 na da kwallon 8 a tarihinsa na Gasar Kofin Duniya.

A minti na 91 kuma,bayan karin lokaci, Mbappe ya kara ta uku.

Ana cikin karin lokacin ne Robert Lewondoaki na Poland ya farke kwallon daya a minti 9, aka tashi 3-1.

Hakan dai na nufin yanzu Poland ta shiga sawun kasashen da suka nade buzunsu zuwa gida gasar ta 2022.

A wasan na ranar Lahadi, Faransa ce ta yi kakagida wajen rike kwallo da kashi 47, Poland kuma 41, a yayin da suka yi kankankan a kashi 12.

Faransa ta kai hari 17 gidan Poland, 8 daga ciki sun tafi daidai, a yayin da Poland ta kai hari 10, amma 2 daga ciki ne suka tafi daidai.

Nan gaba ake sa ran fara wasan Senegal da Birtaniya a zagaye na ’Yan 16.