Za a sanyawa Mali takunkumi idan ta gaza sako sojojin Ivory Coast – Ecowas

0
91

Shugabannin kasashen yammacin Afirka sun shaidawa gwamnatin mulkin sojin Mali da ta sako sojojin Ivory Coast 46 da aka kama a watan Yuli ko kuma a kakaba wa kasar takunkumi.

“Muna rokon hukumomin kasar Mali da su sako sojojin Ivory Coast nan da ranar 1 ga watan Junairu, 2023,” in ji Omar Alieu Touray, shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS, da yake shaidawa manema labarai a wani taro da kungiyar ta gudanar a Abujan Najeriya.

Jami’in diflomasiyyar na kasar Gambia Touray ya kuma ce kungiyar kasashen yammacin Afirka na da damar daukar mataki idan ba a sako sojojin ba nan da ranar 1 ga watan Janairu.

“Idan har Mali ta gaza yin hakan, Ecowas za ta kakaba mata takunkumi,” in ji Omar Alieu Touray.

Ecowas ta ce, shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe, wanda ke shiga tsakani tsakanin Mali da Ivory Coast kan wannan batu, zai je kasar Mali domin neman a sako sojojin.