Babban Sufeton ‘Yan sandan Najeriya ya ce ya ba da umarnin tura jami’an tsaro ɗauke da makamai don ƙarfafa matakan tsaro a sufurin jirgin ƙasa da zai dawo bakin aiki daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin, 5 ga watan Disambar, 2022.
Rundunar ta ce ta tura jami’anta na sashen ‘yan sandan kwantar da tarzoma da sashen ‘yan sanda masu aiki da karnuka da na ofishin tattara bayanan sirri da sashen kula da ababen fashewa, sai kuma rundunar ‘yan sandan kula da sufurin jirgin ƙasa don fara wannan jigila ta jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna.
Yanzu dai hukumomi sun ce sun tura k’arin jami’an tsaro da kayan aiki don ci gaba da sufurin jirgin k’asan Abuja.
Rundunar ‘yan sandan kasar a cikin wata sanarwa da ta wallafa a ranar Lahadi ta ce an tura jami’an nata ne zuwa manyan tashoshin jirgin da cikin tarago-tarago na jiragen da ke bin hanyar Abuja zuwa Kaduna don tabbatar da tsaron fasinjoji da dukiyarsu har ma da daukacin harkar sufurin a kokarin kare aukuwar duk wani abin k’i nan gaba.