Fitacciyar mawakiya Hamsou Garba ta rasu tana da shekaru 63

0
118

Allah ya yi wa shahrarriyar mawakiyar Jamhuriyar Nijar Hamsou Garba rasuwa a cikin daren lahadi zuwa wayewar garin litinin 5 ga watan disamba, tana da shekaru 63 a duniya.

Hajiya Hamsou Garba, ‘yar asalin jihar Maradi ce, amma ta share mafi yawan rayuwar ta ce a birnin Yamai fadar gwamnatin kasar ta Nijar a matsayin mawakiya da ke amfani da kayan kida irin na gargajiya.

Da farko dai ta fara wake-wake ne a karkashin tsarin da ake kira da suna ‘’Samariya’’ tsakanin shekarun 1970 zuwa 1980 a cikin kungiyoy daban daban, kafin daga bisani ta kafa tata kungiya a matsayin mai rera wakoki da suka shafi kishi da kuma son kasa.

Duk da cewa a wasu lokuta ta kasance daya daga cikin mawakan da ke tallata manufofin jam’iyyar siyasa ta MNSD Nasara, amma daga bisani Hajiya Hamsou, wadda ke da kusanci sosai da tsohon Firaministan kasar Hama Amadou, ta ci gaba da yi wa jam’iyyar MODEN/FA Lumana da tsohon firaministan ya kafa wakoki.

To sai dai duk da haka, har zuwa lokacin rasuwar ta, Hajiya Hamsou Garba da ake kira Madame Maiga, ta ci gaba da rere wakoki a game da kishin kasar Nijar da kuma tattalin al’adu a cikin harsuna daban daban na kasar.