‘Yan Bindiga sun kashe ‘yan sanda uku da karin wasu a Sokoto

0
93

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne, a jiya da yamma, sun kai farmaki kauyen ‘Yarbulutu da ke karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato, inda suka kashe ‘yansanda uku tare da wasu ‘yan kasuwa uku.

Harin ya faru ne da misalin karfe 2:30 na rana a lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari da ministan tsaro Salihi Magashi ke Sakkwato suna halartar taron shekara-shekara na COAS na 2022.

A cewar wani shaidan gani da ido, ‘yan bindigar da suka zo kan babura sun bude wuta kan ‘yan kasuwar da ba su ji ba ba su gani ba a kasuwar mako-mako, lamarin da ya sanya mutane tserewa, inda suka yi kaca-kaca da kasuwar

Jami’an ‘yansandan da ke wani shingen binciken ababen hawa sun garzaya wurin da ‘yan bindigar nan take suka kashe ‘yansanda uku tare da kone wasu motoci guda biyu.

Da yake tabbatar da harin, kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Sakkwato, DSP Sanusi Abubakar, ya ce rundunar ta samu rahoton kuma suna farautar maharan domin fuskantar shari’a.

Wani mazaunin kauyen da lamarin ya faru a kan idonsa ya bayyana damuwarsa kan yadda ‘yan bindiga ke ta’addanci a yankin a kullum ba tare da wata turjiya ba.

Ya ce an dade ana tsare da kananan hukumomin Sabon Birni da Isa da ke gabashin Sakkwato domin karbar kudin fansa daga ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ke aiki a Zamfara da kuma wani bangare na Jihar Sakkwato.

“Na tabbata wadannan ‘yan bindigar sun fito ne daga Jihar Zamfara kuma yanzu sun koma yankinmu kamar yadda yankin ke da iyaka da jihar a gabas,” in ji ganau.

Idan ba a manta ba a makon jiya ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari tare da kashe mutane shida a wani kauye na karamar hukumar Goronyo a jihar.

Irin wannan al’amari ya faru a farkon shekarar da ta gabata inda wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kashe sama da mutane 40.