Iran ta zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane da aka samu da laifin yi wa Isra’ila aiki

0
92

Mutane hudu da aka bayyana sunayen su da Hossein Ordoukhanzadeh, Shahin Imani Mahmoudabad, Milad Ashrafi Atbatan, da Manouchehr Shahbandi Bojandi, an rataye su ne da sanyin safiyar Lahadi.

Ma’aikatar shari’ar ta kira su da ’yan daba kuma ta ce jami’an leken asirin Isra’ila ne ke jagorantar su a lokacin da suke lalata dukiyoyin jama’a, sata, garkuwa da mutane da sauransu.

A cewar ma’aikatar shari’ar, dukkan mutanen suna da tarihin aikata laifuka, masu alaka da Ordoukhanzadeh wanda ake zargi da alaka da Mossad, mutumin da aka daure a Kasar Girka tsakanin 2014 zuwa 2017 saboda yunkurin safarar mutane daga Turkiyya zuwa Girka.

An yi zargin cewa sun karbi kudade ne ta hanyar amfani da kudin dijital tare da sayen makamai da kayan aiki a lokacin da suke karbar horo kan yadda za su lalata na’urorin daukar bayanai, da musayar motoci, lamarin da ma’aikatar shari’ar Iran ta ce ya kara jaddada hakikanin yadda suke aiki karkashin ikon Mossad.

An mika tuhumar mutanen hudun ne ga kotun koli, wacce ta tabbatar da hukuncin da aka yanke a ranar Lahadi.