An kai hari da jirgi mara matuki a filin ajiyar jiragen Rasha

0
149

Wani jirgin mara matuki ya kai hari a filin jirgin sama a yankin Kursk na kasar Rasha mai iyaka da kasar Ukraine, kwana guda bayan da Moscow ta zargi Ukraine da kai hare-hare a wasu filayen jiragen saman Rasha guda biyu.

Gwamnan yankin Roman Starovort yace, wata tankar ajiyar mai ta kama da wuta, sakamakon harin amma ba a samu asarar rai ba, suna kokarin shawo kan gobarar.

Sai dai Starovoyt bai yi bayanin inda jirgi mara matukin ya samo asali ba.

A ranar Litinin, ma’aikatr tsaron Rasha ta ce Ukrainee ta yi yunkurin kai wani harin sama a filin jirgin saman a Dyagilevo a yankin Ryazan, da kuma na Engel a yankin Saratov da jirgi mara matuki kirar tsohuwar Tarayyar Soviet.

Ma’aikatar tsaron ta ce an dakile harin jirgi mara matukin, amma ya fadi ya tarwatse a filayen.

Ta ce an kashe sojoji 3, kana 4 sun samu rauni.