Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce za ta shafe kwana 40 ta na rabon katin shaidar rajistar zaɓe (PVC), daga ranar Litinin, 12 ga Disamba.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na INEC, Festus Okoye ya ce a cikin wata sanarwa za a ci gaba da aikin raba katin har zuwa ranar Lahadi, 22 ga Janairu, 2023.
Ya ce daga ranar 6 zuwa 15 ga Janairu, 2023, za a koma ana rabawa a mazaɓu 8,809 na faɗin ƙasar nan.
Ya ce: “Amma daga ranar 15 ga Janairu, za a koma rabon katin a ofisoshin INEC da ke ƙananan hukumomi 774 na faɗin ƙasar nan. Za a ci gaba da rabon har a ranar 22 ga Janairu, 2023.”
Okoye ya ce za a fara rabon katin tun daga ƙarfe 9 na safe har zuwa ƙarfe 3 na yamma, a kowace rana, har da ranakun Asabar da Lahadi.
Za a yi zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.