Gwamnan Kebbi ya bada tallafin N30m ga yan gudun hijira

0
92

Gwamna Atiku Bagudu na Kebbi a ranar Asabar ya bayar da tallafin Naira miliyan 30 ga mutanen da ‘yan bindiga suka raba da gidajensu a karamar hukumar Sakaba ta jihar

Gwamnan ya kuma bayar da gudunmawar tireloli guda biyu na shinkafa domin rabawa ‘yan gudun hijirar domin rage musu radadin kuncin rayuwa.

Gwamnan wanda ya yi jawabi a wajen gabatar da kayayyakin a kauyen Dankolo da ke karamar hukumar Sakaba, ya ce gwamnati ta dukufa wajen dawo da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.

Bagudu, shi ma Shugaban kungiyar Gwamnonin APC, ya ce gwamnati ta dauki matakan da suka dace don mayar da mutanen da suka rasa matsugunansu zuwa gidajen kakanninsu don ba su damar ci gaba da rayuwarsu ta yau da kullun.

Ya kuma bukace su da su zama jakadun zaman lafiya, yana mai jaddada cewa tsaro wani nauyi ne da ya rataya a wuyansa wanda ke bukatar tsarin hadin gwiwa.

Ya ce: “Ina gargadin ku da ku daina yada labaran karya, domin hakan zai kara ta’azzara matsalar tsaro a jihar.

“Duk da haka, ya kamata mutane su ba da sahihan bayanan sirri ga hukumomin tsaro da nufin murkushe laifuka da aikata laifuka.

“Na yi farin ciki da ingantuwar yanayin tsaro a nan da sauran sassan jihar, hakan zai dore.
“Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen ganin cewa mutanen jihar sun kwana da idanuwansu biyu tare da gudanar da ayyukansu na halal ba tare da wani shamaki ba.”

Yayin da yake yabawa hukumomin tsaro, al’umma da malaman addini bisa kokarin da suke yi na samar da zaman lafiya da tsaro, Bagudu ya bukaci ‘yan banga, matasa da kungiyoyin sa kai da su ci gaba da kokarinsu na inganta tsaro a jihar

Gwamnan ya yi alkawarin taimaka wa jama’a da kayan masarufi domin su samu damar gudanar da ayyukan noman rani, sannan ya umurci dan kwangilar da ke tafiyar da aikin hanyar Sakaba – Dankolo, da ya koma wurin domin tabbatar da kammala shi a kan kari.

Tun da farko shugaban karamar hukumar Sakaba Dauda Muhammad-Zaure ya godewa gwamnan bisa cika alkawarin da ya dauka na zuwa kauyen Dankolo domin duba aikin hanyar.

Ya yabawa gwamnan bisa tallafin kayayyakin agaji ga ‘yan gudun hijirar, inda ya kara da cewa hakan zai rage musu radadi.

A nasu jawabin, Hakimin Dankolo, Malam Ibrahim Musa; Ubankasar Sakaba, Malam Garba Musa da Hakimin Wasagu, Malam Muktar Muhammad sun godewa gwamnan bisa wannan tallafi na jin kai.
Shugabannin al’ummar sun kuma bayyana jin dadinsu kan yadda tsaro ya inganta a yankin.