Kasashen G7 za su kafa hukumar tara kudaden tallafa wa Ukraine

0
110

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya  ce kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki ta G7 ta amince da batun kafa wata hukumar da za ta tattara taimako na kudi ga Ukraine, gabanin wani taro a kan sake gina kasar da Rasha ta mamaye a birnin Paris.

Scholz, wanda yake bayani bayan taron da kungiyar G7 ta yi ta kafar bidiyo ya ce, burinsu shine kafa wannan hukumar cikin hanzari,  tare da hadin gwiwar ukraine, cibiyoyin kudi na kasa da kasa da sauran abokan hulda.

Shugaba Ukraine, Volodymyr Zelensky shi ma ya samu shiga wannan taro wanda aka yi a jajibirin  taron da ke tafe a birnin Paris, inda za a duba bukatun Ukraine na gaggawa duba da yadda yanai na tsananin sanyi ke karatowa.

Scholz ya ce ana iya kwatanta wannan shiri na sake gina  Ukraine da irin wanda Amurka ta bijiro da shi bayan barnar da aka yi a yakin duniya na 2.

Wata sanarwa daga fadar gwamnatin Amurka ta ce shugabannin kasashen G7 din sun sha alwashin yin  amfani da hukumar mai siffofin gidauniya, wajen kula da jerin ayyuka  na gajere da dogon lokaci don bada kwarin gwiwa a kokarin sake gina Ukraine.