Argentina ta lashe Kofin Duniya karo na uku

0
148

Lionel Messi ya ja ragamar Argentina ta lashe Kofin Duniya a Qatar, bayan nasara a kan Faransa a bugun fenariti a wasan da ya kayatar a tarihi.

Sun tashi wasan 3-3 har da karin lokaci da ya kai minti 120 daga baya Argentina ta dauki kofin kuma na farko a wajen Messi na uku a Argentina.

Argentina ta fara cin kwallo ta hannun Lionel Messi a bugun fenariti, sannan ta kara na biyu ta hannun Angel Di Maria.

Saura minti 10 a tashi wasan Faransa ta zare daya ta hannun Kylian Mbappe a bugun daga kai sai mai tsaron raga, sannan ya kara na biyu a minti daya tsakani.

A karin lokaci Messi ya kara kwallo daga baya Mbappe ya farke da ta kai ga bugun fenarti, bayan da suka tashi 3-3.

Daga nan Faransa ta lashe kofin da ci 4-2 ta dauki na uku jumulla, bayan wanda ta dauka a 1978 da kuma 1986.

Kylian Mbappe ne ya lashe kyautar takalmin zinare, wanda ya ci takwas a Qatar, Messi ne na biyu mai bakwai a raga.

Golan Argentina Emiliano Martinez shi ne ya karbi kyautar gwarzon mai tsaron raga a Qatar.

Lautaro Martinez mai taka leda a Inter, shi ne matashin dan wasa a Gasar da aka kammala a Qatar – Messi kuwa shi ne fitatcen dan wasan Gasar.

Sai dai Messi shi ne kan gaba a yawan buga wasa a babar Gasar tamaula ta duniya, wanda ya yi fafatawa 26 jumulla – wasa na karshe da ya buga kuma.

Jumulla Messi ya ci kwallo 26 a manyan gasar da ya yi wa Argentina, kenan 13 a Gasar Kofin Duniya da 13 a Copa America ya haura Ronaldo mai 25.

Kociyan Argentina, Lionel Scaloni ya zama na uku da ya lashe Copa America a 2021 da Kofin Duniya a 2022 – wadanda suka yi wannan bajintar sun hada da Mário Zagallo Kofin Duniya a 1970 da Copa America a 1997 da kuma Carlos Alberto Parreira da ya ci Kofin Duniya a 1994 da Copa America a 2004.

An ci kwallo 172 a Gasar da aka yi a Qatar a 2022, ita ce kan gaba da aka zura da yawa a raga, bayan da aka ci 171 a 1998 da kuma a 2014.