Hotunan wasu ‘yan kasar China bakwai da aka kubutar, bayan makwanni 24 dayin garkuwa dasu

0
96

Dakarun sojojin saman Najeriya na musamman sun ceto wasu ‘yan kasar China 7 daga hannun ‘yan ta’adda a jihar Kaduna bayan shafe watanni 5 suna garkuwa da su.

‘Yan ta’addan sun sace ‘yan kasar China ne a wurin hakar ma’adanai da ke Ajata-Aboki, gundumar Gurmana ta karamar hukumar Shiroro a Jihar Neja a watan Yunin shekarar 2022, in ji Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar sojojin saman Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet.

.