Kotu ta bayyana Mohammad Abacha a matsayin dan takarar gwamnan PDP a Kano

0
77

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano a ranar Alhamis ta tabbatar da Mohammad Sani Abacha a matsayin zababben dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano.

Solacebase ta ruwaito cewa alkalin kotun mai shari’a A.M Liman a wani hukunci da ya yanke a yammacin ranar Alhamis ya soke zaben fidda gwanin da ya tsayar da Sadik Aminu Wali a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano na PDP.

Alkalin ya kuma umarci INEC da ta cire sunansa ta musanya shi da Mohammad Sani Abacha.

An yanke hukuncin ne da misalin karfe 12:00 na rana a yau amma daga baya aka canza sheka zuwa karfe 4:00 na yamma.

Kotun ta amince da dukkan shaidar wanda ya shigar da karar.

Wanda ya shigar da karar shine Mohammed Sani Abacha yayin da wadanda ake kara su ne Sadik Aminu Wali, INEC, da PDP.