Manyan Hafsoshin sojin kasashen ECOWAS ko CEDEAO sun gudanar da taro a Guinea Bissau domin kafa Runduna ta musamman don tunkarar ta’addanci da matsalolin juyin mulki da suka addabi yankin.
Wannan na zuwa ne, bayan bayyana matsalolin da suka addabi kasashe mambobin kungiyar, kamar yadda taron Abuja ya amince a yi.
Manufar wannan runduna ta musamman dai kamar yadda taron shugabannin kungiyar ya amince a Abuja, itace samar da tsaron kasashen, ciki har da kula da muhimman wurare da tattara bayanan sirri, da kai dauki tare da tunkarar matsalolin da ke haifar da juyin Mulki.
Manyan hafsoshin na kasashen yammacin Afirka, yayin kammala taron su a Bissau, sun ce kafa sabuwar rundunar abu ne mai matukar wuya, la’akari da wasu batutuwa biyu da suka danganci manufar kafa ta.
Abu na farko a cewar su shine amincewar wasu kasashen a jibge masu irin wadannan dakaru, musamman wadanda wannan lamari ya shafa kai tsaye, da kudin daukar nauyin gudanar da wannan aiki, da kuma dorewarsa.
Sai dai akwai wasi-wasi kan yadda za a tunkari matsalar juyin mulki, musamman idan al’umma suka goyi bayan sojoji da suka jogarance su.
Kasashen Mali da Burkina Faso da Guinea da wannan batu yafi shafa dai sun kauracewa taron.